Uncategorized

BIDIYO: An Ragewa Wani Dan Sanda Matsayi Bayan Ya Gama Tiqan Rawa A Dandalin Tiktok

BIDIYO: An Ragewa Wani Dan Sanda Matsayi Bayan Ya Gama Tiqan Rawa A Dandalin Tiktok

Wani Dansanda a Najeriya mai suna Isaak Mathew ya fuskanci gagarumar matsala, bayan ya gama tiqan rawa a wani bidiyo da aka wallafa a dandalin Tiktok, bayan bidiyo ya watsu a wasu kafafen sada zumunta.

Kamar Yadda zaku gani a bidiyon dake kasa, Dansandan dai ya fuskanci hukuncin ne bayan da aka maka shi a kotu, aka kuma yi shara’a. Daga bisani aka yanke masa hukunci kan abinda ya shuka a shafin na tiktok.

A yanzu haka dai dansandan mai mukamin Kofur, ya dawo Kurtun dansanda a sakamon laifin rawar da ya tika a Tiktok.

Sai dai mutane da dama sun baiyana ra’ayinsu akai bayan ganin wannan hukunci da aka yankewa wannan dan sanda.

Inda wasu ke roko da a sassauta masa, maimakon rage mai muqamin adai yankemai wani hukuncin ba wannan ba.

Ga dai cikakken rahoton nan a kasa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button