Kannywood News

BIDIYO: Anfitar Da Wani Faifan Bidiyon Ummi Rahab Cikin Wani Yanayin Da Bai Kamata A Fitar Ba

KAWAYE SUNCI AMANAR UMMI RAHAB

Anfitar Da Wani Faifan Bidiyo Na Jaruma Ummi Rahab Cikin Wani Yanayin Da Bai Kamata A Fitar Ba.

Kamar Yadda Zaku Gani A Cikin Bidiyon Dake Kasa, Bidiyon Dai Har Yanzu Bai Gama Karade Shafukan Sada Zumunta Ba.

Sai Dai Datti Assalafiy Wanda Shine Ya Wallafa Bayanin A Shafinsa Na Sada Zumuntar Facebook Yace.

“Nima na ga bidiyon Jarumar Kannywood Ummi Rahab a wani yanayin da bai kamata ba, wasu kawayenta sun mata bidiyo kuma suka fitar da bidiyon saboda tsabagen cin amana.

Makiya suna neman tarwatsa rayuwar wannan yarinya marainiya, Wallahi da tayi aure da yafi mata alheri akan wannan rayuwar yaudara cikin fim da take yi.

Hakika cin amana tayi yawa a wannan rayuwa, abu mai wahala a wannan zamanin namu shine gane hakikanin masoyi na gaskiya.

Duk wanda aka cutar dashi a yau ko akaci amanarsa to akwai sa hannun na kusa da shi wato aboki ko kawa, wani lokacin har da dan uwa na jini.

Muna rokon Allah Ya nesanta tsakanin mu da masoyan karya, Ya karemu daga sharrin makiya na fili da na boye.

Ga Bidiyon Nan Ku Kalli Karin Bayani

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button