News

BIDIYO: Bidiyon Yadda ƴan-Banga Suka Cafke ƴan ISWAP Takwas 8 A Jahar Neja

BIDIYO: Bidiyon Yadda ƴan-Banga Suka Cafke ƴan ISWAP Takwas 8 A Jahar Neja

Jami’an tsaro na ƴan-banga da matasa sun kama wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne tare da mika su ga hukumomin tsaro a jihar Neja.

Jaridar PRNigeria cewa, an kama wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne a yayin wani sumame na bincike da tambayoyi a gundumar Wawa da ke New Bussa.

Wata majiya da a ka yi sumamen da Ita, a cikin wani faifan murya da aka aika wa PRNigeria ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun amsa laifinsu a cikin al’umma.

Majiyar ta ce: “Muna godiya ga Allah bisa kokarin da sojoji suke yi a yankinmu. A wani bangare na bincikenmu na tsaro, bayan yunkurin kai hari a sansanin soji da ke Wawa kwanan nan, mun shiga neman wasu baki a unguwarmu, inda muka samu nasarar cafke su takwas da niyyar aikata laifi, tare da kwato bindigogi kirar AK-47, gidan ake harsashi 10, da harsashi 160 da sauran muggan makamai.

“Abin mamaki ma har wasu daga cikin wadanda ake zargin sun yi sallar asuba tare da mu a masallaci. Ba wanda zai yi tunanin cewa su masu laifi ne, domin kamanninsu na ustazai ne,” inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button