Kannywood News

BIDIYO: Bidiyon Yadda Mawaki Rarara Ya Shirya Addu’a Ta Musamman Akan Rashin Tsaro A Nigeria

BIDIYO: Bidiyon Yadda Mawaki Rarara Ya Shirya Addu’a Ta Musamman Akan Rashin Tsaro A Nigeria

Shahararren mawakin siyasar nan na Hausa, Dauda Adamu Kahutu, wanda a ka fi sani da Rarara, ya shirya addu’a ta musamman a kan rashin tsaro da ke addabar Arewaci da ma wasu sassa na Nijeriya.

An shirya addu’ar ne a Jihar Kano a yau Litinin, da zimmar Allah Ya kawo ƙarshen rashin tsaro a ƙasar.

Da ya ke jawabi a yayin taron addu’ar, Rarara ya ce ya zama wajibi a haɗu a yi wa ƙasa addu’a a bisa mawuyacin halin da ta tsinci kanta.

A cewar sa, rashin tsaron da ya addabi Arewa da ma wasu sassa a ƙasar nan, na matukar bukatar addu’a, musamman ma yadda babban zaɓe na 2023 ke tunkaro wa.

Ya ƙara da cewa Musulmai da Kiristoci ya kamata su duƙufa da addu’a a masallatai da coci-coci domin neman ɗauki daga Ubangiji.

Rarara ya kuma ce taron bashi da wata alaƙa da siyasa, “illa dai a nemo mafita a wajen Ubangiji domin samun zaman lafiya.

“Idan babu zaman lafiya, ko mu ma ba za mu iya yin harkar fim ɗin mu ba. Saboda haka muna kira ga ƴan Nijeriya, Musulmai da Kiristoci, da mu dage da addu’a a masallatai, coci-coci da kuma gida-gida domin Allah Ya bamu zaman lafiya,”in ji Rarara

.

Ya kuma ƙara da cewa taron ya yi amfani wajen kara danƙon zumunci tsakanin ƴan masana’antar Kannywood.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa an yi saukar Alkur’ani da kuma yanka raƙumai guda biyu, inda a ka yi sadakar naman domin Allah Ya karɓi addu’ar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button