News

Gaskiyar Magana Ta Fito Akan Kama Sheikh Bello Yabo Hukumar Dss Tayi Saboda Ya Soki Gwamnatin Buhari

Gaskiyar Magana Ta Fito Akan Kama Sheikh Bello Yabo Hukumar Dss Tayi Saboda Ya Soki Gwamnatin Buhari.

LABARIN AN KAMA SHEIKH BELLO YABO SOKOTO

Yanzu nake karanta labari da ake yadawa a Facebook cewa jami’an tsaro DSS sun kama babban Malamin Musulunci, dodon marassa gaskiya da miyagun Shugabanni a Nigeria Sheikh Bello Yabo Sokoto (H)

Kafin nayi nayi wannan rubutun; sai da na kira daya daga cikin manyan Daliban Malam Ballo Yabo inda ya tabbatar min da cewa DSS ba su kama Malam ba, yanzu haka Malam yana gida cikin iyalansa yana shirin karatun da zai gabatar yau, don haka labarin kamashi ba gaskiya bane.

Abinda ya faru wasu suke cewa an kama Malam shine, a karatun da Malam ya gabatar jiya, ya caccaki Kakakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wato Garba Shehu wanda yace bidiyon da masu garkuwa da mutane suka fitar suna dukan mutanen da suka kama wai farfagandace.

To shine Malam Bello Yabo Sokoto ya mayarwa Garba Shehu zazzafan raddi a jiya, har yayi fatan Allah Ya sa masu garkuwa da mutanen su cafke Garba Shehu su kaishi sansani su masa duka, daga nan sai ace bidiyon Farfagandace yaji inda dadi.

Sheikh Bello ya tabbatar da Garba Shehu a matsayin daya daga cikin mutanen da suke cin amanar shugaba Buhari ta hanyar boye masa gaskiyar abinda yake faruwa.

Tabbas duk wanda ya saurari maganganun zai ji a ransa cewa da kyar idan ba’a tura hukuma sun kama Malam Bello ba.

Muna rokon Allah Ya tsare mana rayuwar Malam Bello Yabo, Allah Ya kara masa taimako da nasara da cikakken kariya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button