Uncategorized

BIDIYO: Bidiyon Yadda ‘Yan Kungiyar Sintiri (Vigilante) Da Ake Zargi Da Kashe Wani Malamin Makarantar Allo A Kano Unguwar Dabai,

BIDIYO: Bidiyon Yadda ‘Yan Kungiyar Sintiri (Vigilante) Da Ake Zargi Da Kashe Wani Malamin Makarantar Allo A Kano Unguwar Dabai,

Ana zargin ‘yan kungiyar sintiri (vigilante) da kashe wani malamin makarantar allo a unguwar Dabai, da ke karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Shi dai Musa Mai-Almajirai, sanannen malamin Qur’ani ne a unguwar, inda yake da daruruwan almajirai.

Ana zargin ‘yan kungiyar sintirin da yi wa malamin dukan tsiya a ofishinsu bayan da aka kai shi can bisa zargin da wata mata ta yi masa na yunkurin satar yaro.

Jaridar Premium Times ta intanet ta ruwaito cewa dan malamin, Ibrahim ya sheda mata cewa, ”Mahaifin nasa yana tafiya ne sai ya ji kukan jariri sabuwar haihuwa a wata bola.

Sai ya je ya dauki yaron, sai kawai wata mata ta yi masa ihu, tana ce masa barawon yaro.”

”Kururuwar da matar ta yi ce ta janyo ‘yan kungiyar sintirin da sauran jama’ar unguwar wadanda suka rufe shi da duka,” in ji dan.

Ya kara da cewa, ”Daga nan sai suka tafi da shi ofishinsu suka ci gaba da dukansa. Daga baya ya fadi ya suma.”

Ya ce,” Bayan da wasu ‘yan unguwar suka gane shi sai suka garzaya da shi asibiti, inda ya cika a hanya.”

Dan malamin ya sheda wa jaridar cewa ‘yan-sanda sun kama shugaban ‘yan-sintirin na unguwar, mai suna Munkaila, inda ake bincikensa a caji ofis na Rijiyar Zaki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button