News

Bidiyon Haduwar Gwamna Ganduje Da Tsohon Sarkin Kano, Khalifa Sanusi II, A Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe Dake Abuja, Ranar Litinin.

Bidiyon Haduwar Gwamna Ganduje Da Tsohon Sarkin Kano, Khalifa Sanusi II, A Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe Dake Abuja, Ranar Litinin.

Wannan shi ne karon farko da aka ga mutanen biyu tare tun bayan da Ganduje ya tube Sarki Sanusi a shekarar 2020.

A cikin wani gajeren faifan bidiyo da ke daukar ganawar tasu, ana iya ganin tsohon sarki da Ganduje suna gaisawa a wani dakin shakatawa da ke filin jirgin.

Gwamnan ya tsige sarkin ne a ranar 9 ga Maris, 2020, saboda abin da ya bayyana a matsayin “rashin mutunta umarnin da ya dace daga ofishin gwamna”.

An kuma dauke Sanusi daga Kano aka tura shi zuwa Loko, wani yanki mai nisa a jihar Nasarawa, yayin da ake bin diddigin kudaden masarautar da ke karkashinsa.

Bayan shekara guda, gwamnan ya ce ya dauki matakin ne domin ceto tsarin sarautar jihar daga cin zarafi.

Da yake jawabi a wani taron gabatar da wani littafi kan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda wani dan jarida, Mista Bonaventure Melah ya rubuta, Ganduje ya ce Sanusi ba shi ne mutumin da ya fi dacewa da karagar sarautar ba, inda ya yi zargin cewa an nada tsohon sarkin ne saboda cusawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan haushi.

A watan Afrilun 2014 ne Jonathan ya tsige Sanusi daga mukamin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) saboda ikirarin da ya yi cewa wasu shugabanni a karkashin gwamnatin Jonathan sun sace dala biliyan 49.

Da yake nuna rashin jin dadinsa kan yadda Sanusi ya fito fili kan badakalar da ake zarginsa da aikatawa, Ganduje ya ce ya kamata tsohon gwamnan na CBN ya tattauna batun a asirce da tsohon shugaban kasar wanda shi kuma zai iya ba da umarnin gudanar da bincike kan zargin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button