Kannywood News

Bidiyoyin Cikin Dankareren Gidan Da Jaruma Sadiya Haruna Ta Ginawa Mahaifiyarta

Bidiyoyin Cikin Dankareren Gidan Da Jaruma Sadiya Haruna Ta Ginawa Mahaifiyarta

Fitacciyar Jarumar Kannywood, Sadiya Haruna ta gwangwaje mahaifiyarta da wani katafaren gida na alfarma.

Jaruma Sadiya ta sanyawa kowani bangaren kayan alatu kama daga gadaje da kujeru na zamani, harda na’urar sanyaya
waje.

Bidiyoyin ciki da wajen dankareren gidan ya bayyana a shafin jarumar na soshiyal midiya

Jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kuma mai daukar hankali a kafafen sada Zumunta ta Instagram, wato Sayyada Sadiya Haruna, ta gwangwaje mahaifiyarta.

Sadiya ta dankarawa mahaifiyar tata wani katafaren gida domin ta more tare da cin ribar haihuwarta da tayi.

Sau da dama jarumar ta sha fitowa tana bayyana irin soyayyar da take yiwa mahaifanta musamman ma mamar tata.

Sannan ta sha cewa a kullun cikin yi mata addu’a suke don haka ita ma take son farin cikinsu.

https://www.instagram.com/reel/CgrsfAAoses/?igshid=YmMyMTA2M2Y=

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button