Uncategorized

BIDIYO: Dubun Wani Matashi Da Ya Bude Account Da Sunan Wata Budurwa Sannan Yake Damfarar Mutane A Social Media Ya Cika

BIDIYO: Dubun Wani Matashi Da Ya Bude Account Da Sunan Wata Budurwa Sannan Yake Damfarar Mutane A Social Media Ya Cika

YADDA DUBUN DAN DANFARA MUSA L MAJE TA CIKA HAR AKA KAMA SHI.

Game da yadda aka yi nasarar cafke musa L maje Saurayi da ya shahara yana danfarar mata har ma da maza, da wani Facebook account din bogi mai suna Zahra Mansur.

Wani mutum yaga guntun bidiyon wata mata a wayar Musa. Musa ya dauki bidiyon ne cikin rashin sanin matar. Bidiyon gashin kantane bata kulle ba yagani a wayan musa, amma ba wani bidiyo bane da yake bayyana tsiraici sosai, amma dai dole ta dau mataki in ta gani.

To a ranar Talata ne labarin ganin video yazo ma matar, Wani ne ya kira ta ya shaida mata cewa ya ga bidiyonta a wayar Musa, inda hankalinta ya tashi ta rasa ya zatai kuma bata so ta masa magana kai tsaye.

Sai ta nimi taimakon wani mutum ta sanar da shi ba tare da shi musa ya san cewa an gaya mata ba, sai wanda aka gaya mawa ya yanke shawarar tunkarar shi ta hanyar kai shi ga hukuma ba tare da saninsa ba, kuma bazasu bari ya saniba to amma suna bukatar dubarar yadda zasuyi masa, shi ne Muka ce wa matar ta kira shi ta gaya masa tana Kano tana son ganinsa. Daman musa nasan ganin yasake haduwa da ita, jin wannan labarin na cewa zai hadu da matan nan, har yana ce mata shifa ya kosa su hadu!

A daren Talata ne ta buga masa waya. Kuma shi wanda aka gayamawa ya taimaka mata suka tafi Kano ranar Laraba da sassafe. Saboda muhimmancin lamarin, kuma basaso su rasa musa, basa so a samu matsala, Kama musa nada Muhimmanci sosai a wajan su, so sun isa Kano da wuri a ranar laraba.

A takaice an kama musa tare da jami’an yan sanda da mutanan da sukaje Kano da matar da taimakon wasu mutane, musa ya gigice da ya ganshi a hannun hukuma kuma suma wa yanda sukai rakiyar sun gigice bisa ganin yadda musa yazo hannu,

‘Yan sandan cikin ladabi da kwanciyar hankali sun tambaye shi bidiyon amma ya musanta. Ya musanta duk zargin da ake masa, yace babu wani bidiyo mai kama da na matar a wayar shi, da yanda suka bincika wayansa ne fa anan ne a kaga bidiyon, Nan Musa ya fara kuka yana nadama Yana neman gafarar matar.

Yan sanda suka cigaba da binciken wayan tare da matar da sauran mutanan, shi ne fa a lokacin ne aka samu tsiraicin mata da yawa (hotuna da bidiyo) a wayarsa. “INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN ”

Abin mamakin ganin fuskokin wasu mutane da suke da kima da daraja a cikin bidiyon, mutane ne da aka sansu sosai a Facebook mutane ne da arewa Facebook ta sansu wajan fade aji,

Anan ne aka gano cewa Zahra Mansur account ne na bogi (fake account), kuma Musa shi ne mai amfani da wannan account din. Ya kasance yana amfani da wannan account din don damfarar maza da mata anan Facebook.

Wani abin mamaki da bakinciki shi ne ganin yadda maza ke tura masa kudi. Hasali ma, da yawa wadanda ake kiransu Facebook elite (influencers) Na tura masa kudi, Abin mamaki kamar yadda aka ce. A halin yanzu yana tare da ‘yan sanda. Baza’a ambaci sunayen matan da aka gani a wayarsa ba. Haka nan baza’a kira sunayen mutanen da ya damfara da fake account ba.

Amma tabbas zuwa yanzu duk wanda ya damfara suna nan hankalinsu ya tashi, kuma tabbas dayawan mazan da suka turawa musa tsiraicinsu hankalinsu ya tashi, kuma abun kunyane tabbas garesu, ya kamata kowa ya gyara yasan kalar mu’amalar da zai dungayi a Facebook.

Dazun iyayen Zahra mansur sun tasa musa maje a gaba Dan gayamusu ya akai yake amfani da bank account mai suna Zahra mansur da Facebook account yana damfara, har an nuno fuskan Zahra da kanta tana cewa mahaifinta ya tambaye shi ina yasamu information dinta???

Ana sa ran a gobe in Allah ya kaimu gobe yan sanda zasuyi masa video su watsa da irin hanyoyin dayake bi wajan damfarar mutane,

Muna fata wannan zai zama izina ga alummarmu mata da zama na Facebook.

Daga Usman Rabiu kwankwaso.

https://youtu.be/TDtn54todT8

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button