News

BIDIYO: Gwamnatin Nigeria Ta Wanke Abba Kyari Bisa Zargin Halasta Kudin Haram Na Alakanta Shi Da Hushpuppi

Gwamnatin Nigeria Ta Wanke Abba Kyari Bisa Zargin Halasta Kudin Haram Na Alakanta Shi Da Hushpuppi

DAGA Datti Assalafiy

Maigirma Ministan Shari’ah kuma babban Lauyan Gwamnatin Tarayyar Nigeria Dattijon kirki Abubakar Malami, SAN bayan ya karanci sakamakon binciken case din Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari karkashin jagorancin marigayi DIG Joseph Egbunike akan zargin karban cin hanci daga Hushpuppi, Ministan ya mayar wa shugaban ‘yan sanda amsa a rubuce cikin takarda mai dauke da reference number kamar haka: DPPA/LA/814/21.

A cikin takardan wanda ya fito daga ofishin Maigirma Ministan Shari’ah sashin gabatar da kara Department of Public Prosecution (DPP) wanda sune suke nazarin dukkan kararraki a ofishin Ministan Shari’ah karkashin jagorancin Director of Public Prosecution Barrister Muhammad Abubakar, sunce DCP Abba Kyari bai aikata laifin karban cin hanci daga Hushpuppi ba, don haka bai da wata tuhuma akan wannan shari’a.

An zargi Abba Kyari akan wadannan laifuka kamar haka
-Criminal conspiracy
-Aiding and abetting Internet fraud
-Wire fraud
-Identity Theft
-Money laundering
Sashin gabatar da kara daga Ofishin Maigirma Ministan Shari’ah sunce babu laifi daya da Abba Kyari ya aikata

Malami Ya rubutawa IGP takarda kamar haka:
”Ina sanar da kai cewa bayan dogon nazari da lura akan batun shari’ar Abba Kyari da Hushpuppi inda kukace an gano an tura kudi cikin wadannan account number : 2255416115 Zenith Bank mallakin Usman Ibrahim Waziri, 0130665392 Guaranty Trust Bank mallakin Adekoye Sikiru, 2080537566 Zenith Bank mallakin Hussein Ala, da kuma kudin da aka tura wa wata mata mai suna Sharon Festus, dukkan kudaden da aka tura cikin account din, masu account din sun cire kudin sunyi amfani dashi, lura da haka wannan bai shafi Abba Kyari ba, babu wata shaida kai tsaye ko shaida karkatacciya da ta nuna yana da laifi anan, kuma masu account number din sun zo sun bada shaida sun tabbatar basu da wata alaka da Abba Kyari kudin su ne..”

A cikin takardan da Ministan Shari’ah ya rubutawa shugaban ‘yan sanda, ya bada shawara wa IGP akan ya tsawatar ko ya hukunta DCP Abba Kyari bisa wasu kura-kurai ko laifuka da yayi guda biyu wanda sukaci karo da dokokin aiki, kuskure na farko shine Abba Kyari ya kama wani mutum ya tsare na tsawon wata guda ba tare da ya kaishi kotu ba, sannan sai yunkurin kare kansa da yayi a shafinsa na facebook ba tare da ya karbi umarnin shugaban ‘yan sanda ba

Alhamdulillah Jama’a ku tayamu murna, Sarkin Yakin Nigeria yayi nasara akan wannan case din da taron dangin maciya amana da wakilan ‘yan Biyafara suka hadu suka kulla masa, sukace yana da alaka da gawurtaccen dan damfara Hushpuppi domin su huce takaicin kawar da Kwamandojin yakin Biyafara da yayi bayan sun dawo daga karban horon soji a Kasar Izraa’ilah.

Insha Allah kamar yadda Sarkin Yaki yayi nasara akan wannan haka zaiyi nasara akan makircin da aka kulla masa a NDLEA.

Muna rokon Allah Ya taimaki gaskiya akan karya da makirci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button