Kannywood News

BIDIYO: Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un Yanzu-Yanzu Allah Yaiwa Yakubu Kafi Gwamna Rasuwa.

BIDIYO: Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un Yanzu-Yanzu Allah Yaiwa Yakubu Kafi Gwamna Rasuwa.

Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu Yanzu Daga Shafin Jaridar Kannywood News Na Cewa, Allah Yayiwa Yakubu Kafi Gwamna Rasuwa

Kamar Yadda Shafin Dokin Karfe Suka Wallafa A Shafin Su Na Facebokk Cewa.

Allah yayiwa Alh umar malunfashi rasuwa wanda akafi sani da kafi gomna nashirin kwana chasa’in.

Muna Addu’a Allah ya gafarta masa kurakurensa idan tamu tazo Allah kasa muchika da inami Allahumma Ameeen.

CUTA BA MUTUWA BA SAI KWANA YA ƘARE, KALAMAN MARIGAYIN NA KARSHE A ZANTARWAR SA DA MUJALLAR FIM

TSOHON ɗan wasan kwaikwayon nan Alhaji Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura) ya bayyana cewa ya na buƙatar addu’a daga al’ummar Annabi saboda yanayin rashin lafiyar da ya ke ciki, wanda ya kai har an kwantar da shi tsawon lokaci a Pinnacle Special Hospital da ke unguwar Hausawa kusa da Masallacin Murtala ia jihar Kano, inda ya ke kwance magashiyan.

Bankaura, wanda a yanzu ake kira Yakubu Ka-Fi-Gwamna saboda rol ɗin sa a diramar ‘Kwana Casa’in’ ta gidan talbijin na Arewa24, ya na daga cikin daɗaɗɗun ‘yan wasan kwaikwayo da Arewa ke ji da su, domin ya fara dirama ne tun kafin a assasa masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.

Yayin da wakilin mujallar Fim ya ziyarce shi Bankaura ya ce, “Kuma dai ka ga a yadda ka same ni. Kuma ina fatan ku ci gaba da yi mani addu’a; Allah shi ya san yadda zai yi da bayin sa.”

Ubangiji Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa, Idan Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button