Uncategorized

BIDIYO: Jaruma Saratu Gidado Daso Ta Fashe Da Kuka Acikin Kotu Bayan Ta Kawo Karar Delegates Din Da Suka Cinye Mata Kudi

BIDIYO: Jaruma Saratu Gidado Daso Ta Fashe Da Kuka Acikin Kotu Bayan Ta Kawo Karar Delegates Din Da Suka Cinye Mata Kudi

Allah sarki Fitacciyar Jarumar Kannywood Saratu Daso ta fashe da kuka inda takawo karar Delegates kotu bayan sun cinye mata kudi Kuma Daga Baya suka ki zabarta.

Kamar Yadda Zaku Gani Acikin Wannan Bidiyon Dake Kasa, Jarumar Ta Fashe Da Kuka Tare Da Rokon Kotu Da Tabi Mata Hakkin Ta.

Jarumar masana’antar shirya fina finan hausa ta Kannywood Saratu Daso takawo kara gaban wata babbar kotu acikin garin kano kan cinye mata kudade da delegates sukayi.

Idan dai baku manta ba cikin wani bidiyo da jarumar ta wallafa a shafinta na sada zumunta, jaruma dasu ta baiwa delegates awanni ashirin da hudu da su gaggauta dawo mata da kudinta ko ta makasu a gaban kuliya.

Saidai ayau kwatsam sai ganin jarumar akayi tsaye a gaban wata kotu a jahar kano inda take fadin cewar tazo babbar kotu domin tashigar da kara kan cinye mata kudaden da akayi sannan kuma ba’a zabeta ba.

Ga video

https://www.instagram.com/tv/CeThHMxjbjo/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button