Uncategorized

Da Dumi-dumi: Kotu Ta Samar Wa Malam Abduljabbar Lawya Bayan Hukumar Bada Agajin Shari’a Sun Ki Tsaya Masa A Shari’a.

Kotu Ta Samar Wa Malam Abduljabbar Lawya Bayan Hukumar Bada Agajin Shari’a Sun Ki Tsaya Masa A Shari’a.

Aliyu Samba

A safiyar yau ne a ka cigaba da sauraren shari’ar malamin addinin muslunci Sheikh Abduljabbar Kabara a babbar kotun shariar muslunci dake zaman ta kofar kudu. A zaman na yau, Lawyoyin gwamnati 10 ne suka bayyana a matsayin masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barr Yakubu Abdullahi


A daya bangaren, Lawyoyin hukumar bada agajin shari’a ta legal aid council sun turo da wakilcin Barr Muktar Labaran Usman tare da Barr M.S Muhammad, inda suka bayyanawa kotu cewa sun aiko da takardar martani ga umarnin da kotu tayi musu na tsayawa wanda ake kara a kotun.

“Munzo bisa gayyatar kotu, kuma mun mayar da martani a rubuce a takarda dan bada fahimtar mu akan gayyatar da kotu tayi a ranar 23/5/22, kuma rejistiran wannan kotu ya sa hannu ya karba a ranar 24/5/22” Inji Barr Muktar Labaran

Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya bayyana cewa kotu ta karbi wannan takardar sannan tayi umarnin a karanta abinda ke kunshe a cikin ta a cikin kotu.

Takardar tace: “Hukumar bada agajin shari’a (Legal aid council) hukuma ce ta gwamnatin tarayya, wacce take bada agajin shari’a ga mutumin da a wata baya samun sama da mafi karancin albashi (Minimum wage) Naira 30,000, kuma bisa nazarin da muka yi akan wanda ake kara, yana samun sama da haka a duk wata. Sannan laifin da ake tuhumar wanda ake kara a wannan kotu, laifin batanci ne ga Annabawa, kamar yadda sashe na 8 karamin sashe na 2 na dokar bada agajin shari’a ya shimfida, laifin sa baya daga jerin laifuffukan da muke iya tsayawa mutum a kotu”

Wanda ake kara Malam Abduljabbar Kabara, yayi suka kan fadin Legal aid council cewa yana daukar albashi sama da Naira 30,000, ya bayyana cewa shi ba ma’aikaci bane kuma baya daukar albashi.

A nasu martanim, Lawyoyin legal aid sun bayyanawa kotu cewa doka ce ta basu cikakkiyar damar da zasu iya auna mutum, kuma abinda ya bayyana garesu shine hatta tufafin da ke jikin wanda ake kara, ya nuna cewa shi ba mabukaci bane.

Anan ne lawyoyi masu gabatar da kara ta bakin Barr Yakubu Abdullahi ya roki kotu da ta Umarci Kwamishinan Sharia na jihar kano ya baiwa wanda ake kara lawyan da zai tsaya masa a kotu, dogaro da sashe na 389 ACJL 2019 da ta ce kwamishinan sharian na cikakken iko a jihar ya samar da lawya ga wanda ake kara.

Malam Abduljabbar ya koka matuka da rashin nutsuwa da rokon da lawyan gwamnati yayi cewa kwamishinan shari’a ya sama masa lawya, ya bayyana cewa bashi da aminci da hakan domin Gwamna ne ya nada Kwamishinan, kuma karara anji gwamnan yana kiran sa da dan akuya da ya aika zuwa mayanka.

“A matsayin shi na Attoni Janar na jihar kano wanda gwamnan Jihar kano ya nada shi, shi kuma gwamnan kano bayan an rufe ni a gidan gyaran hali kafin a fara shari’a ya fada a video yana cewa, (Da ya zaci ni sa ne, to amma daga baya sai yaga a she dan akuya ne, dan haka yayi umarnin a kaini kurkuku, kar magriba tayi face ina kurkuku, ya kaini mayanka” Inji Malam Abduljabbar.

Malamin ya sake jaddawa kotu cewa rashin aminci tsakanin sa da lawyoyi ya faru ne sakamakon yadda Lawyan sa na farko ya ci amanar sa, ya bayyana cewa lawyan nashi na farko Barr Rabiu Abdullahi ya matsa masa akan ya karbi takardar shedar asibitin mahaukata amma yaki, sannan yace dashi wani ma’aikacin gwamnati mai suna Baffa Babba Dan Agundi (Shugaban Hukumar Karota na jihar Kano) yayi masa alkawarin Naira Miliyan 100 muddin ya yarda ya bayyana wa duniya cewa Malam Abduljabbar ya gagara kare kansa a wajen mukabala.

A wannan karon Barr Rabiu ya mike a cikin kotu inda ya roki kotu a matsayin sa na lawya da aka ambace shi a wannan gabar shari’ar, da ta shigar da wannan ambatar sunan sa da Malamin yayi a rubuce da tuhumar da yayi masa saboda zai shigar da karar Malamin bisa wadannan kalmomi da yayi a hakkin sa.

Bayan kotu ta saurari dukkan bangarorin, Mai shari’a Alkali Ibrahim Sarki yola ya bayyana cewa babu inda dokar ACJL tace a bawa kwamishinan shari’a na jihar kano damar ya bawa wanda ake kara lawya, abinda dokar tace shine kotu ta samar wa wanda ake kara lawya.

Ya kuma bayyana matsayar sa akan takardar da legal aid council suka aiko na martani da fahimtar su bisa doka, inda ya ce ya amince da hakan, kuma ya sallame su.

Kotun ta kuma bada umarnin cewa a zama na gaba, lawya mai zaman kansa Barr Dalhatu Shehu Usman ya bayyana a kotu dan tsayawa wanda ake kara, ya kuma dage zaman shari’ar zuwa 9/6/2022.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button