Uncategorized

BIDIYO: Musulimci Ya Samu Qaruwa Masha Allah, Wata Mata Mai Zaman Kanta A Kasar Indonesiya Ta Amshi Addini

BIDIYO: Musulimci Ya Samu Qaruwa Masha Allah, Wata Mata Mai Zaman Kanta A Kasar Indonesiya Ta Amshi Addini

Allahu Akbar

Wannan Matashin Malami Mai Suna Ustaz ebit lew Kullum bashi da Aiki Sai bi lungu da saqo Yana Shiga Club-Club, wajajen Shaqatawa a Garin Jakarta daka qasar Indonesiya yana Musu Da’awar Addinin Musulunci,

Yanayin Da’awar Tasa Ne Cikin hikima da Nuna Tausasawa da Kalamai masu daɗi ba Zagi ba ƙyama, Zai Iya Zuwa ya Samu gayu suna Zaune suna Shan Wiwi a Jangul ɗin Su Kuma yaje yayi Musu Sallama har su gaggaisa Sannan Ya samu waje ya Zauna a Cikin su ya fara Musu da’awa, in Kuma ya Lura ga wani ko Wasu wanda ba Musulmi bane Kuma ya/Suna Cikin halin rashi Matuqa Sai Yaje ya same su gaisa wani ɗakin Zaka ga kwaline kawai aka ɗan Bubbuga aka yi rumfa haka Zai Shiga ya Zauna ayi hira Ayi raha Ya ɗauki Kuɗi ya basu sannan Ya ɗora Musu da da’awar,

Wannan Matar da Kuke gani Duk Jikin ta a Zane Yake da Zane (Tatu), Irin Sana’ar da Take Yi Kafin Akai Mata Da’awa ba Sai an Faɗa Maka ba, Amma Allah Ya Shirye ta Ta karɓi Musulunci Ta hanyar Wannan Mai Da’awa da Tausasawa,

Bayan Ta saka Kammallen Hijabi Ita kanta bata San Sadda ta fashe da Kuka ba a Lokaci Guda Kuma Tana nadamar Ayyukan ta na Baya.

Hmmm Wata miyar sai a maqota,
Ya Kamata Wasu malaman mu a Nan Nijar da Najeriya su Fahimci bafa da Zage-zage da kafirtarwa Ko Zafin Kai ake da’awa ba, bal Da Tausasawa me da kyautatawa da kusantar wanda kake Son isarwa da da’awar ka.

إن الله و ملإكته يصلون على النبي يا أيها الذين آمنو صلوا عليه و سلموا تسليما🍒

اللهم صلى على محمد و آل محمد
#جمعہ__مبارک
#جمعة

Mallam BaQeer ✍️
Friday/Jun/23

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button