Kannywood News

BIDIYO: Nayi Saukar Alqur’ani Mai Girma, Amma Ban Gama Secondary Ba- A Cewar Murja A Gaban Yan Sanda

BIDIYO: Nayi Saukar Alqur’ani Mai Girma, Amma Ban Gama Secondary Ba- A Cewar Murja A Gaban Yan Sanda

Cikin Wani Bidiyo Da Jarumar Tiktok Murja Ibrahim Kunya Tai Bayani A Gaban Yan Sanda.

Ta Baiyana Cewa Tayi Saukar Alqur’ani Mai Girma amma bata kammala karatun ta na boko ba.

Idan baku manta ba a jiya lahadi ne murja ta shirya yin bikin birthday din din ta, sai dai yan sanda sun kama ta ana tsaka da shirye shiryen.

Rundunar Ƴan Sandan jihar Kano ta kama fitacciyar mai barkwancin nan ta #TikTok Murja Ibrahim Kunya.

Koda ya ke Ƴan sandan ba su yi ƙarin bayani ba, amma idan zaku iya tunawa a shekarar da ta gabata ne wani lauya ya shigar da ƙorafi inda yake neman da a binciki Murja da wasu fitattun mawaƙa da masu amfani da TikTok kan zargin ɓata tarbiyya.

An kama Murjar ne yayin da take tsaka da shirye-shiryen shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Rundunar ƴan sandan Kano ta ce, ta kama Murja Ibrahim Kunya bayan ƙorafin da Zauren Malaman Kano suka yi a kanta da wasu masu amfani da TikTok.

Wata majiya ta ƙara da cewa tuni manyan mutane suka shiga sahun neman a saki Murjan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button