Uncategorized

BIDIYO: Rundunar Yansanda Sunyi Nasarar Chafke Wanda Ya Kashe Wata Mata A Dakin Hotel Ya Gudo Kano.

BIDIYO: Rundunar Yansanda Sunyi Nasarar Chafke Wanda Ya Kashe Wata Mata A Dakin Hotel Ya Gudo Kano.

‘Yan sanda na jihar Kebbi sun cafke wanda ya kashe wata mata a Otal

Daga Comrd Yusha’u Garba Shanga.

Rundunar Yan sandan jihar Kebbi ta kama Bashir Mohammed dan shekara 22 wanda ake zargin ya kashe Jennifer Goje a garin Zuru.

Jennifer ta rasa ranta ne a dakinta da ke River Side Hotel a Unguwar Zuru ranar Juma’a 3 ga watan Yuni 2022. An sami gawarta kwance cikin jini tare da raunukan sukan wuka a wasu sassa a jikinta cewar wata majiya.

Kakakin rundunar yansandan jihar Kebbi SP Nafi’u Abubakar ya ce

“Tabbas mun kama wanda ake zargi ya kashe matar. Jami’an mu sun bi shi har Kano aka kamo shi, aka dawo da shi Zuru, daga bisani aka kawo shi Shelkwatar yansandan jihar Kebbi varin Birnin kebbi, kuma ana gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuka SCID”.

Yanzu dai binciken yansanda ne kadai zai tabbatar da hakikanin abin da ya faru har Wanda ake zargi ya kashe Jennifer.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button