Uncategorized

BIDIYO: Wani Ya Je Fadar Gwamnatin Katsina Da Tabarya Domin Daukar Fansar Mahaifiyarsa Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe

BIDIYO: Wani Ya Je Fadar Gwamnatin Katsina Da Tabarya Domin Daukar Fansar Mahaifiyarsa Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe

A jiya Alhamis ne wani ya shiga gidan gwamnatin Katsina da tabarya da nufin ya zo daukar fansa aka kisan da ‘yan bindiga suka yi wa Mahaifiyarsa.

Majiyar RARIYA ta bayyaa mana cewa sai da matashin ya shiga har cikin harabar fadar gwamnatin kafin jami’an tsaro da ke bakin kofa suka ankare da me ya kawo sa. Inda bayan ya shiga har ciki sai suka kama shi suka yi ta dukansa.

Bayan Jami’an tsaron sun gama dukan sa sai suke tambayar sa me ya kawo sa a nan? Sai yake fada masu cewa ‘yan bindiga sun shiga har kauyen su sun kashe Mahaifiyar sa shine ya zo daukar fansa.

Daga bisani dai jami’an ‘yan sanda sun yi yunkurin kai shi ofishin su, amma sai wani daga cikin masu baiwa Gwamna Masari shawara ya umarci da a mika shi ga Jami’an SSS su je su yi bincike akansa.

A lokacin da matashin ya shigo fadar gwamntin, Gwamna Masari ba ya gari, Sakataren fadar gwamnatin ne kadai ke a cikin Gwamnatin da wasu Kwamishinoni.

Abin tambaya dai a nan shine, akan wa ya zo daukar fansar a fadar ta Gwamnatin Jihar Katsina?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button