Uncategorized

BIDIYO: Yadda Aka Kwantar Da Mutane Sama Da 200 A Asibitoci Daban-daban Yayin Da Wasu Yan Jaribola Suka Bude Wata Tukunyar Gas Mai Dauke Da Guba A Kano

Aka Kwantar Da Mutane Sama Da Mutane 200 A Asibitoci Daban-daban Yayin Da Wasu Yan Jaribola Suka Bude Wata Tukunyar Gas Mai Dauke da wani sinadarin da ba a san ko menene ba a unguwar Sharada ta jihar Kano.

Shugaban asibitin kwararru na Murtala Muhammad, Dr. Hussaini Muhammad ya bayyana cewa an kawo mutane 69 asibitin kuma sun cigaba da karbar wasu.

A halin yanzu wadanda abin ya shafa suna sashen gaggawa na asibitin ana kula da lafiyarsu Sakamakon yadda Suka jikkata, saboda da suke samun sarkewar numfashi ba.

Har yanzu dai ba a gano sinadarin ba amma mutanen yankin sun bayyana cewa yana yaduwa a cikin iska ya yi illa sosai ga mazauna yankin na unguwar mundadu da makwaftan su.

Wannan dai na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da fashewar wata tukunyar gas a unguwar Sheka inda ya kashe mutane biyu tare da jikkata sama da mutane 19.

Muna roko a taya su addu’a. Allah ya kiyaye faruwar hakan a gaba.

– Rahma

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button