Uncategorized

BIDIYO: Yanzu-yanzu: Matasa sun k*he wani mutumi Musulmi Kan Kalaman Batanci Ga Manzon Allah (SAW) A Abuja

Yanzu-yanzu: Matasa sun kashe wani mutumi Musulmi Kan Kalaman Batanci Ga Manzon Allah (SAW) A Abuja

Wasu matasa a ranar Asabar sun hallaka wani dan kungiyar Bijilante kan zargin kalaman batanci ga Man.

Rahotanni Sun Baiyana cewa an hallaka dan Bijilantin ne a sashen yan Timba dake kasuwar kayan itace a unguwar FHA Lugbe.

Rahoton Jaridar Punch Ya baiyana cewa shaidun gani da ido yace dan Bijilantin Musulmi ne kuma ya shahara da zagin manzon Allah. amma yayi wani sabo da daren jiya.

A riwayar Daily Trust, bayan kalaman batancin, sai ya gudu ya nemi mafaka a Ofishin yan Bijilanti dake kasuwar misalin karfe 1 na rana.

An tattaro cewa a wannan lokacin fusatattun matasa suka kure masa gudu suka fito da shi karfi da yaji daga cikin ofishin kuma suka kasheshi kai tsaye, daga baya suka konashi.

Wani dan kasuwa a wajen mai suna Halilu yace: “Sunan mutumin Small Hundaru, wannan ba shine karon farko da zai zagi annabi ba.”

An damkeshi yana kokarin sayen abinci a kasuwa da rana, saboda lokacin da yayi batancin, babu mutane sosai a wajen, sai aka buga masa ice a akai. Sai da aka kwace bindigar hannunsa suka lallasa shi.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button