Uncategorized

Bidiyo: Yadda Aka Titsiye Wani Dan Sanda Yana Tsaka Da Busa Tabar Wiwi A Wani Kango

Bidiyo: Yadda Aka Titsiye Wani Dan Sanda Yana Tsaka Da Busa Tabar Wiwi A Wani Kango

Wani bidiyon dan sanda dake ta yawo a shafukan sada zumunta, inda acikin bidiyon aka ga wani dan sanda nata busa tabar wiwi.

An kama wani dan sanda yana tsaka da busar tabar wiwi a wani kango wanda ya fi kama da gulbi sanye da kayan aikinsa, LIB ta ruwaito.

Hukumar ‘yan sandan kasar Ghana ta bayyana dan sandan a matsayin Sajan Isaac Sowah Nii na ofishin ‘yan sandan Accra.

Kamar yadda hukumar ‘yan sandan ta saki takarda, yanzu haka ana ci gaba da bincike kuma da zarar an kammala za a hukunta Sajan din bayan gurfanar da shi gaban kotu.

Ga bidiyon a kasa:

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button