Uncategorized

BIDIYO: Yanzu-Yanzun Anfara Zanga Zangar A Saki Sheikh Abduljabbar A Babban Masallacin Abuja

BIDIYO: Yanzu-Yanzun Anfara Zanga Zangar A Saki Sheikh Abduljabbar A Babban Masallacin Abuja

Cikin Wani Bidiyo Da Zaku Kalla Na Yadda Wasu Gungun Mutane Da Suka Fita Zanga Zangar A Saki Abduljabbar.

Acikin Bidiyon Zakuji Yadda Yadda Suke Kare Abduljabbar Tare Da Yin Kira Da A Gaggauta Sakin Malamin.

Yanzu Yanzun nan Mabiya Shi’a Suna Gudanar Da Zanga Zangar a Saki Sheikh Abduljabbar a Babban Masallacin Abuja

Wasu mabiya shia suke gudanar da Zanga Zangar dole sai an saki Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Izuwa Yanzu dai kowa yasan cewa an riga an Yankewa Sheikh Abduljabbar Hukuncin Kisa kuma ta Hanyar rataya a wata kotun Musulunci dake a jahar kano bayan da aka kamasa da laifin yin batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Sai dai bayan yanke hukuncin ne sai daliban Sheikh Abduljabbar sukace basu yadda da Hukuncin ba don haka zasu daukaka kara izuwa kotun koli.

A jiya Alhamis ne mabiya shi’a suka Fitar da wata takarda wacce ke dauke sa Gargadin cewa a gaggauta sakin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara Wanda kuma a yau Juma’a suka fara Gudanar da Zanga Zangar a saketa domin a ganin su baiyi laifin da ake tuhumar sa dashi na wanda yasa har aka yanke masa hukunci.

Ga Cikakken Bidiyon Yadda Sukai Zanza Zangar A Birnin Tarayya Abuja.

https://youtu.be/2aJUI9WKfH0

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button