News

BIDIYO:Mun Sauke Malam Saboda Mun Faɗa Masa Abinda Muke So Ya Riƙa Faɗa A Huɗuba Amma Ya Ƙi – Inji Sanata Ɗansadau

Mun Sauke Malam Saboda Mun Faɗa Masa Abinda Muke So Ya Riƙa Faɗa A Huɗuba Amma Ya Ƙi – Inji Sanata Ɗansadau

Abba Hikima ya wallafa a shafinsa cewa, “yanzu nake ji a BBC Hausa daga bakin wani Sanata Dansadau (shugaban kwamitin masallacin.

Yan majalisu na Apo) cewa dalilin da yasa suka sauke Sheikh Nuru Khalid shine yana tsoma baki a cikin harkokin siyasa kuma wai hakan ba aikin sa bane. Sannan wai sun gaya masa abun da suke so ya dinga fada a khutba kuma yaki.

Wannan ita ce daya daga cikin hanyoyin da yan siyasa marasa daraja suke amfani da ita wajen wasa da kwakwalen mutane.

Su nuna cewa duk da muhimmancin siyasa da yan siyasa a cikin rayuwar alumma, da kuma kazantar su, to su kadai ya kamata su yita.

Idan bamu chanja wannan tunanin ba, har abada abubuwa baza su gyaru ba.

https://youtu.be/pwFCDITRbL4

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button