Kannywood News

Bidiyon Yadda Matan Shirin Izzar So Suka Rushe Da Kuka Yayin Ziyarar Da Suka Kai Kabarin Daraktan Tan Shirin A Kabarin Sa

Bidiyon Yadda Matan Shirin Izzar So Suka Rushe Da Kuka Yayin Ziyarar Da Suka Kai Kabarin Daraktantan Shirin Nura Mustapha Waye.

Allah sarki. Hakika mutuwa wani babban tabo ne wanda yake fitowa a cikin zuciya, kuma baya tafiya har abada.

Matan shirin Izzar So sun kai ziyara ta musamman, zuwa ga Kabarin Darakta Nura Mustafa Waye, wanda Allah Ya karbi rayuwar sa kwana hudu da suka wuce.

Bayan jiya anyi sadakar uku, yau kuma Juma’a abokan sana’ar sa mata sunyi ayari sun shiga har cikin Makabartar da aka binne shi, domin su ziyarce shi.

A yayin ziyarar wasu da dama daga cikin matan sun fashe da kuka, kuma an gabatar da addu’o’i, na neman Rahmar Allah a gare shi.

Ga dai bidiyon ziyarar nan a kasa, kamar yanda muka samu daga tashar Duniyar Kannywood

https://youtu.be/J9YbwAqKHQo

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button