News

Bidiyon Yadda Yan Bindiga Suka Kai Hari Wani Gida A Funtua Don Sace Mutane Amma Suka Gamu Da Gaban Su

Bidiyon Yadda Yan Bindiga Suka Kai Hari Wani Gida A Funtua Don Sace Mutane Amma Suka Gamu Da Gaban Su

Yadda Yan Bindiga Suka Kai Hari Wani Gida A Funtua Don Sace Mutane Amma Suka Gamu Da ‘Bakin Ciki’

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kutsa gidajen mutane a Funtua a daren ranar Juma’a sun sace wasu amma sun gaza shiga wani gida.

Kama Yadda Wani faifan bidiyo da aka nada da na’urar daukan bidiyo na sirri ta CCTV ta nuna yadda yan bindigan suka so shiga wani gida amma suka kasa.

Wani abokin mai gidan da suka kasa shigan ya ce mai gidan da iyalansa suna Abuja amma ya hada na’urar ta CCTV da wayarsa don haka ya ga abin da ya faru.

Daily Nigerian ta tattaro cewa yan bindigan ba su yi nasarar cimma burinsu ba a wani gida inda suka tarar da masu gidan sun tafi Abuja.

A cewar Ahmed Abdulkadir, abokin mai gidan (an boye sunansa), bayan sun yi harbi a kofar, sun shiga cikin gidan amma ba su tarar da kowa ba.

Ga Bidiyon Nan 👇👇👇

Mista Abdulkadir, wani tsohon direkta na NBC, ya rubuta a shafinsa na Facebook: “Sun balle kofar gidan misalin karfe 10.20 na dare kamar yadda agogon CCTV kyamara ya nuna.

Inda Ya Kara Da Cewa “An gode Allah, abokina da iyalansa ba su gari kuma mai gadin da ya lura ba lafiya sai ya tsere gidajen makwabta. “Abokina, wanda injiniya ne da lantarki kuma ya san harkar sadarwa ta zamani, ya saka na’urar CCTV a gidansa wanda ke nuna masa komai a wayansa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button