News

CIGIYA: Attajirar mata a Abuja tana neman kyakkyawan namijin da zai ɗirka mata ciki ta ba shi N3m

CIGIYA: Attajirar mata a Abuja tana neman kyakkyawan namijin da zai ɗirka mata ciki ta ba shi N3m

Wata mata mai dukiya da ke zama a garin Abuja wacce bata taɓa haihuwa ba tana cigiyar namiji mai kyau da zai ɗirka mata ciki, Legit.ng ta ruwaito.

Wata fitacciyar ma’abociya amfani da shafin sada zumuntar zamani, Uwaoma Susan Joseph ce ta bayyana wa duniya wannan kudirin na matar a Facebook inda ta adana bayani akanta saboda tsaro.

Yayin da matar take nema, ba kyauta zai yi mata wannan gagarumin aikin ba, akwai Naira miliyan uku (N3,000,000) da ta yanke shawarar za ta bai wa wanda ya cancanci su yi wannan harkar da shi kuma ya aiwatar da komai lafiya.

Susan ta bayyana cewa za a rufe masa idanu da kyalle ne, ta yadda ba zai san wacce zai yi lamarin da ita ba.

Sannan za a samar masa da ɗaki ne musamman a otal, wanda za su dinga al’amarin babu dare babu rana har sai an tabbatar ta samu juna biyu.

A cewarta, da zarar asibiti sun tabbatar da ta samu cikin, daga nan ne yaci waɗannan maƙudan kudade, Allah barshi za a iya sallamarsa.

A cewar Suzy, dalilin kuwa rufe masa ido yana da alaƙa da kada nan gaba ya lallaɓo yana buƙatar a ba shi ɗansa. Kamar yadda Suzy ta wallafa saƙon matar a shafinta:

“Suzy ki temaka ki wallafa min. “Ina buƙatar kyakkyawan namiji. Za a rufe masa idanu da ƙyalle a lokacin da za mu sadu don in ɗauki ciki. Bayan komai ya kammala zan biya shi kuɗinsa ya ƙara gaba.

“Za a rufe masa idanunsa ne saboda kada ya dawo yana neman ɗansa nan gaba. Kuma za mu ci gaba da komai har sai an tabbatar ina da ciki sannan ne zai tafi.

“A lokacin zan ba shi sallamar aikin da yayi min. Kuma zai bar inda nake a Abuja, ni zan ɗauki nauyin duk wani kuɗi da za a kashe.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button