Kannywood News

CIKIN BIDIYO: Sarkin Waka Ya Baiwa Ladin Cima Kyautar Miliyan Biyu Taja Jari Yakuma Baiwa Al’umma Hakuri

Dan Allah Ayi Hakuri Wallahi Ban Fadi Wani Abu Dan In Batawa Wani Ko Wata Sana’ar Sa Ba- Cewar Sarkin Waka.

Cikin Wani Faifan Bidiyo Da Fitaccen Mawaki Naziru M. Ahmad Ya Saki, Ya Nemi Mutane Suyi Hakuri Bisa Kalaman Sa.

Mawakin Ya Wallafa Bidiyon Ne A Shafukan Sa Na Sada Zumunta, Inda Ya Roki Al’umma Musamman Ma Mutanen Gari.

Haka Zalika Mawaki Yayi Magana Ga Masu Zaginsa, Inda Ya Kwatanta Abin Da Cewar Dalili Ne, Yana Faruwa Ko Ga Yan Siyasa In Zabe Yazo Sai Kaga Wanda Bai Kai Bama Ya Zagi Shugaban Kasa.

Mawakin Yace A Bidiyon Na Baya Wanda Shine Silar Janyo Cece Kucen, Allah Ya Sani Bai Kama Sunan Wani Ya Zaga Ba.

Duk Wanda Kaji Ya Kira Sunan Sa, To Misali Yai Dashi Ba Zagin Sa Ba.

Sai Yace Amma Shi Duk Wanda Yasan Ya Kama Sunan Sa Ya Zage Shi, Yaje Kawai Yai Baccinsa Da Ido Biyu, Allah Zai Kula Da Wannan.

Na Tabbata Mun Zauna Da Ali Dashi Falalu, Na Lura Gyaran Masana’antar Bazai Gyaru Bane. To Gara Mu Ankarar Da Mutane.

Ita Kuma Waannan Matar Mun Yanke Matsayar Cewa, Zamu Bata Naira Miliyan Biyu Taje Ta Fara Jari Muga Mai Allah Zaiyi.

Indai Neman Abinci Ne Yake Kawota Masana’antar Kannywood To Zamu Tallafa Mata Da Naira Miliyan Biyu Taje Ta Fara Jari.

https://youtu.be/7qC_oDr0yUo

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button