Kannywood News

DA ƊUMI-ƊUMI: Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano ta soke lasisin ƙungiyoyin shirya finafinai dake ƙarƙashin masana’antar Kannywood.

DA ƊUMI-ƊUMI: Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano ta soke lasisin ƙungiyoyin shirya finafinai dake ƙarƙashin masana’antar Kannywood.

Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano ta soke lasisin ƙungiyoyin shirya finafinai dake ƙarƙashin masana’antar Kannywood; tare da lasisin gidajen gala dake nan Kano baki ɗaya.

Kamar Yadda Shugaban Hukumar Abba El-mustapha Ya Sanar A Ranar Juma’a

Tuni Dai Manyan Masu Shirya Fina Finai A Masana’antar Sukai Na’am Da Wannan Mataki Na Shugaban Hukumar.

Inda Babban Mai Shirya Fina Finai Abubakar Bashir Mai Shadda Yai Na’am Da Matakin Tare Da Wallafa Cewa.

Kannywood Babbar Masana’anta ce, kuma uwa ce maba da mama. GASKIYA ya kamata a tsaftace ta da bara gurbi.

Ni Mai Shirya Fim ne, kuma Mai Daukar Nauyi + Na Goyi bayan hakan Dari bisa dari.

Da fatan kowacce kungiya zata yi kokarin tantance mutanen ta.

Allah ya taimaki Kannywood ❤️


@abbaelmustapha1

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button