Uncategorized

Da Dumi-dumi Cikin Bidiyo Sheikh Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo Ya Karyata Jita Jitar Da Ake Alaqantawa Dashi

Da Dumi-dumi Sheikh Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo Ya Karyata Jita Jitar Da Ake Alaqantawa Dashi

Tun bayan wani guntun bidiyo da Sheikh Muhammad Rabi’u R/lemo Ya Wallafa A Shafinsa na sada zumunta.

Wanda acikin bidiyon yake cewa, Ba a addini ba ne ware wata rana a shekara ko wasu ranaku don tunawa da mutuwar wani.

Inda Ya Cigaba Da Cewa, Da addini ne to babu shakka Annabi Muhammadu S.A.W Shi Yafi Cancanta Da A Warewa Wannan Rana.

Wannan bidiyo Da Shehin Malamin Ya Wallafa Ya Tayar Da Kura Tare Da Haifar Da Cece Kuce Musamman Ma A Shafukan Sada Zumunta.

Saboda Anga Wallafar Tazo Dai Dai Da Lokacin Da Yan Shi’a Ke Fita Tattaki Da Nufin Bayyana Bakin Cikin Su Kan Kisan Imam Hussain.

Ana tsaka da wannan cece kuce ne, sai aka hango wata wallafa wadda aka alaqantata da shehin malamin kamar haka.

Yaune malaminmu sheikh ja’afar Adam ya cika shekaru 11 da rasuwa, Allah ya cigaba da karban shahadarsa.

Sai dai malamin yafito tare da nesanta kansa da wancan rubutu inda ya wallafa cewa.

Ba a kawar da gaskiya da karya

Bayan fadakarwar da na yi a wannan kafa cewa ba addini ba ne ware wata rana a shekara don tunawa da mutuwar wani sai yaran dantamore Abduljabbar suka kirkira karya, suka samar da fake account a face book da sunana wai a shekarar 2018 13/April na yi rubuta don tunawa da shahadar Sheikh Ja’afar – Allah ya yi masa rahama – a wannan rana.

Wannan rubutu ba ni na yi shi ba, karya suka jingina min, rubutun ma cike yake da kurakurai na ka’idojin rubutun hausa, duk wanda ya san yadda nake rubutuna ya san ba na tafka irin wadannan kurakurai.

Don haka duk wanda ya ga wannan rubutu ya shaida ba ni na yi shi ba.

Allah ya bar mu a kan gaskiya da yada ta. Ameen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button