![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/04/FB_IMG_1649275234942.jpg?resize=480%2C258&ssl=1)
Da Dumi Dumi: Tsohon Shugaban Kasa Good Luck Jonathan Yayi Hatsari Mutum 2 Sun Mutu
“Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Goodluck Jonathan, Ya Yi Hatsari, Mutum Biyu Cikin Mukarrabannsa Sun Mutu”
![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/04/FB_IMG_1649275389115.jpg?resize=300%2C171&ssl=1)
Hatsarin mota ya rutsa da tsohon shugaban Najeriya
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi ranar Larabar nan a birnin Abuja.
Bayanai dai sun ce hatsarin ya yi sanadin mutuwar mukarraban Jonathan guda biyu.
Lamarin ya auku ne a lokacin da jakadan na musamman da kungiyar ECOWAS ta tura Mali ke kan hanyar zuwa gidansa daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe zuwa gidansa a Abuja.
Daya daga cikin masu taimaka wa tsohon shugaban Najeriya wanda ya tabbatar da aukuwar hatsarin, ya ce mai gidan nasa yana cikin koshin lafiya.