News

DA DUMI-DUMI: Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta aike da Shugaban Hukumar EFCC zuwa Gidan Yarin kuje.

DA DUMI-DUMI: Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta aike da Shugaban Hukumar EFCC zuwa Gidan Yarin kuje.

Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu-Yanzu Na Cewa.

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta samu Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Abdulrasheed Bawa da laifin cin zarafi a kotu.

Alkalin kotun, Chizob Orji, ya kama Abdulrasheed Bawa da laifin saba umurnin da kotun tayi tun shekarun baya.

Saboda haka ya umurci hukumar yan sanda ta damke Abdulrasheed Bawa da gaggawa kuma a jefashi kurkukun Kuje har sai ya bi umurninsa.

Dangane da gazawar hukumarsa na kin bin umurnin da kotu ta bayar a baya na EFCC ta dawo da wani abin da ta kama. Range Rover da Naira Miliyan Arba’in (40,000,000.00) ga wanda ake tuhuma a shari’ar da ke gaban kotu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button