Music

Dan Shahararren Mawaki Davido, Ifeanyi Mai Shekara Uku A Duniya Ya Rasu

Dan Shahararren Mawaki Davido, Ifeanyi Mai Shekara Uku A Duniya Ya Rasu

A shekarar 2018, D’ Banj, ya rasa dansa Daniel mai shekara daya ta irin wannan hanya, inda shi ma ya fada tafkin ninkaya da ke gidan mawakin ya kuma rasa ransa.

Rahotanni daga Najeriya na cewa Ifeanyi, da ga fitaccen mawakin Afrobeat Davido da suka haifa tare da budurwarsa Chioma Rowland ya rasu.

Ifeanyi, wanda shekarunsa uku kacal, ya rasa ransa ne a ranar Litinin, sanadiyyar nutsewa da ya yi a ruwan tafkin ninkaya kamar yadda fitaccen shafin Lindaikejiofficial, ya wallafa a dandalin Instagram.

Lamarin ya faru ne a gidan mawakin da ke unguwar masu hannu da shuni ta Banana Island a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Fitaccen shafin Instablog9na da ke bibiyan al’amuran fannin nishadi a Najeriya, ya ruwaito cewa, Ifeanyi ya kwashe tsawon lokaci a karkashin ruwan tafkin ninkayar, kafin daga bisani a ankara cewa ya nutse a ruwan.

Bayanai sun yi nuni da cewa an bar Ifeanyi ne a hannun masu renonsa a lokacin da lamarin ya faru kuma tuni an kama wasu daga cikinsu.

A cewar rahotanni, Davido ya tafi Ibadan domin halartar wani taron ahalinsa a lokacin da ibtila’in ya auku.

“Mutuwar da ba dadi, wannan labari ya girgiza ni matuka.” Jarumi A.Y. ya wallafa a shafinsa na Instagram.

A makon da ya gabata, Ifeanyi ya cika shekara uku da haihuwa inda mahaifinsa ya wallafa hotonsa tare da taya shi murna.

“Za ka samu daukaka fiye da ni. Ina mai tayaka murnar zagayowar ranar haihuwarka dana.” Davido ya rubuta a shafinsa na Instagram.

Wannan ba shi ne karon farko da irin wannan lamarin ya faru a tsakanin mawakan Najeriya ba, a shekarar 2018, D’ Banj ya rasa dansa Daniel mai shekara daya ta irin wannan hanya, inda shi ma ya fada tafkin ninkaya da ke gidan mawakin ya kuma rasa ransa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button