News

Darajar Wani Rago Ta Fadi, An siyar Da Shi Dubu 300,000

Darajar Wannan Ragon Ta Fadi A Inda Aka Siyar Dashi Dubu 300.000

Alhaji Muntari Getso Shi ne Shugaban kasuwar dabbobi da ke garin Getso a karamar hukumar Gwarzo ta jihar kano,

ya shaidawa wakilinmu cewa a zahirin gaskiya Raguna a wannan shekarar ba suyi daraja yadda ya kamata ba.

wanda hakan ya janyo karyewar darajarsu musamman Ma Raguna.

Inda ya kwatanta cewa sun sayar da wani tikeken bijimin Rago kan kudi Naira dubu Dari uku 300,000.

Wanda ya kamata ace darajarsa tafi haka, amma sakamakon karyewar farashi ba yadda suka iya haka suka daure suka sallamar.

Shugaban kasuwar ya kara da cewa har yanzu da Sallah ke cigaba da gabatowa.

masu niyyar layya da manyan masu kudi basu fito sun taimakawa talaka ba wajen siyan dabbobin yadda yakamata.

Da an sami yadda ake so za a iya siyarda Rago har Naira dubu dari hudu da hamsin 450,000.

Muntari Getso yace a halin da ake ciki makiyaya sunyi babbar asara a wannan shekara.

Domin ko kudin da suke siyawa dabbobin Su abinci basu dawoba ballantana ayi batun riba.

Sai dai kuma har yanzu da yawan mutane na korafin rashin kudi tare da kuma tashin gwauron zabin tashin kayan masarufi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button