News

Davido ya cika alƙawarin raba Naira Miliyan 250 ga gidajen marayu 292 Yayin da Naziru M. Ahmad ya cika alkawarin raba miliyan uku

Davido ya cika alƙawarin raba Naira Miliyan 250 ga gidajen marayu 292

Shahararren mawaƙin nan na Nijeriya, David Adeleke, wanda a ka fi sani da DavidoDavido ya cika alƙawarin da ya ɗauka na raba Naira Miliyan 250 ga gidajen marayu 292 a faɗin ƙasar nan.

A ƙarshen 2021 ne Davido ya sanar da cewa zai raba Naira Miliyan 250 ga gidajen marayu a faɗin ƙasa domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Davido ya baiyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na twitter a jiya Talata da daddare.

Davido ya bada cikakken bayani da sunayen gidajen marayun da su ka amfana da tallafin na sa, inda ya ce gidajen marayu 292 ne su ka amfana.

Mawaƙin ya kuma gode da yabawa ƴan kwamitin da ya kafa su raba tallafin, inda ya ce kwamiti ne cike da mutane zaƙaƙurai da su ka iya aiki.

Ya kuma yabawa magoya bayansa da danginsadanginsa da kuma abokai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button