News

Free Murja Yan Hisba Sun Cafke Murja Ibrahim Kunyan, 8

Free Murja Yan Hisba Sun Cafke Murja Ibrahim Kunyan

Rundunar Hisbah a jihar Kano ta ce ta kama shahararriyar ƴar TikTok din nan Murja Ibrahim Kunya da laifin wallafa wasu abubuwan da ba su dace ba da kuma waɗanda ba na Musulunci ba a shafin sada zumunta na TikTok.

Makwanni biyu da suka gabata, Hisbah ta ƙaddamar da farautar wasu ƴan Tiktok guda shida waɗanda suka ce suna saɓa wa ka’idojin musulunci a kullum wajen amfani da kafafen sada zumunta.

Kakakin Hisbah Lawal Fagge ya shaida wa wakilin Arewa News Eye, cewa an kama Murja Ibrahim Kunya da sanyin safiyar Talata, tare da saurayinta.

Read More

“Jami’anmu sun kama ta ne da karfe 1:00 na rana a gidanta tare da saurayinta, wanda shi ma yana tare da mu.”

Murja
Murja

“A baya dai, makwabtanta sun kawo mana korafi game da halinta. A yanzu haka muna kan bincike kafin daukar mataki na gaba,” inji shi.

Ana zargin Murja da yin amfani da kalaman ɓatanci da rashin kunya a cikin bidiyonta, wanda dubban mutane ke kallo.

Ba ta ce uffan ba kan wannan zargi, amma an gan ta a wani faifan bidiyo da ba a tantance ba yana yawo a shafukan sada zumunta tun bayan kama ta.

A bidiyon, an jiyo ta tana cewa ba ta saci komai ba, kuma ta gode wa Allah a kan hakan.

Kano dai na da mafi yawan al’ummar Musulmi kuma tsarin shari’a na Musulunci yana aiki tare da tsarin doka a jihar.

visit our page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button