Kannywood News

Gaskiyar Batu Kan Auren Ummi Rahab Da Angonta Lillin Baba Allah Ubangiji Yabada Zaman Lafiya

Gaskiyar Batu Kan Auren Ummi Rahab Da Angonta Lillin Baba Allah Ubangiji Yabada Zaman Lafiya

Gamasu kallon fina finan hausa idan aka ambaci sunan Ummi Rahab sunsan wace jaruma ake nufi domin kuwa tana daya daga cikin matasan yan mata jarumai acikin masana’antar Kannywood a wannan lokacin.


Ummi Rahab tsohuwar jarumace acikin masana’antar Kannywood domin kuwa idan mukai la’akari da cewar tara fitowa acikin fina finan hausa tun tanada shekara goma, ga wanda zasu iya tunawa tafito acikin wani film maisuna (Ummi) wanda yawanci wasuma da ummi suke kiranta sakamakon a wancan lokacin shirin yasamu karbuwa awajan mutane daban daban.

Ummi Rahab dai tafara soyayya da mawaki Lilin baba bayan dawowarta masana’antar Kannywood a shekarar data gabata inda film dinta na farko bayan dawowarta shine (farin wata) na kamfanin Adam a zango.

Saidai jim kadan bayan dawowarta masana’antar Kannywood sunsamu matsala da jarumi Adam a zango wanda hartakai Adam a zango ya cireta daga film dinsa maisuna (farin wata) kamar yadda ya fadawa BBC Hausa, haka zalika ya bayyana cewar shi yanzu babu hannunsa akan jarumar.

Saidai kwatsam sai aka fara ganin Ummi Rahab acikin shiri mai dogon zango maisuna (WUFF) mallakin mawakin Hausa Lilin Baba, inda daganan kuma soyayya mai karfi tashiga tsakanin ummi rahab da mawakin wanda yanzu har abu yakai ga aure.


Inda a watan june 06/2022 dazamu shiga ake sa ran Ummi Rahab da Angonta mawaki Lilin Baba zasuyi aure kamar yadda Manajan mawakin kuma daraktan shirin (WUFF) sulaiman sir zeezu ya sanar.

Ya bayyana cewar angama shirye shiryen auren Ummi Rahab da mawaki Lilin Baba a watan gobe dazai kama, saidai ba’a saka ranar ba, gadai cikakken bidiyon domin ku kalla.

Ga video

https://youtu.be/jXeV4bHJdQw

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button