Uncategorized

Gwamnatin Kano za ta fara tura ɗalibai karatu ƙasashen waje a watan Satumba — Abba Gida-Gida

Gwamnatin Kano za ta fara tura ɗalibai karatu ƙasashen waje a watan Satumba — Abba Gida-Gida

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa rukunin farko na ɗaliban da su ka samu nasarar samun tallafin karatu na kasashen waje za su fara karatu a jami’o’i daban-daban nan da watan Satumba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin sakataren yada labaran sa, Hisham Habib ya fitar a Kano a ranar Asabar.

Ya ce Gwamnan ya bayyana hakan ne a gidan gwamnati a lokacin da ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, da ‘yan majalisar masarautar a lokacin bikin Sallah.

Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin sa na baiwa fannin ilimi fifiko.

Yusuf ya godewa sarkin tare da yaba wa irin rawar da sarakunan gargajiya ke takawa a matsayin masu kula da al’adu da yada zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a tsakanin al’umma.

Tun da fari, Sarki Bayero ya yi kira da a samar da taki ga manoma a farashi mai rahusa, da farfado da shuka biahiyu da samar da ruwan sha a jihar.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar da yanayin da zai taimaka wajen kara zuba jari domin ci gaban jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button