Uncategorized

BIDIYO: Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un Asirin Yan Kannywood Ya Tonu Kan Rashin Lafiyar Jarumi Mal. Lawan Dangajere

BIDIYO: Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un Asirin Yan Kannywood Ya Tonu Kan Rashin Lafiyar Jarumi Mal. Lawan Dangajere

Yanzun nan ina Duba videos sai nayi Arba da wannan videon da Aminu Abdullahi yasa wani Ɗan TikTok yana bayani Akan halin da man lawan Ɗan wadan nan na Hausa Film yake ciki Abin Akwai Takaici matuƙa!!

Yayi bayani cewa man lawan shekarar sa biyu chif baya iya Tafiya Domin ƙafarsa baza ta Taku ba sai dai a Ɗauke a Tayar.

Anje Asibiti Ance wani ƙashi ne a bayansa ya sami matsala shine ya taɓa ƙafar tasa Ana neman kuɗin scanning 70k Amma tsawon shekara biyun ba a samu wanda ya taimake shi da wannan kuɗin ba.

Aminu Abdullahi yayi bayani Acikin videon cewa ya Tambayi man lawan shin ya nemi Taimakon wasu kuwa Acikin ƴan Film ɗin?

Sai man lawan yace Eh sosai ma Hadiza Aliyu gabon ita kaɗaice ta taɓa bashi 60k, yaje wajen Ali Nuhu amma ya kama faɗa yace Afuta dashi daga office ɗinsa, sannan lokacin da Adam A zango yazo zaiyi Film ɗin Asin da Asin ya samu labari yasa Aka Ɗakko man lawan har hotel ɗin da yake daya Ganshi Saida yayi kuka daga ƙarshe yabashi 20k yaje ganin Dauda kahutu Rarara shima ya balbale shi da faɗa daƙyar yabashi 3k. Sai kuma Tijjani Gandu wanda lokaci lokaci yakan turomai na Abinchi.

Sai shi Aminu Abdullahi yasake Tambayar man lawan dawa dawa kake ganin da sun sani zasu Taimake ka Amma kuma basu sani ba?

Sai man lawan yace irinsu naziru Sarkin waƙa. To daga ƙarshe dai Aminu Abdullahi ya tuntuɓi irin Abale dasu lawan Ahmad gaba ɗayan su rikici ne ya rabasu suna nuna bazasu taimaka ba. Sai da aka sami SarkinWaka saiya tambaya yanzu me ake buƙata sai akace mai Afun farko 70k na scanning nan take ya turo kuɗin yace kuma idan Anyi scanning ɗin A gayamai Zaici gaba da Taimakawa.

SHARHI…..
wato a Gaskiya a iya sanina babu wasu rukunin jama’a ko wata masana’anta da tara marasa mutunci irin ƴan kannywood! Gashi dai Abubuwa dayawa suna faruwa Acikinsu Amma saisu gaza Taimakawa kuma sunada Damar Taimakon.

Menene Amfanin Ɗaukaka ko samun Dukiyar da wani Bazai Amfana ba? Kuna Ɗibar motoci da manyan gidaje kuna bawa mata, kuna tafiya ƙasashen Duniya shaƙatawa, kuna Duk Abinda kukeso Amma ku gaza Taimakon Ɗan uwanku da 70k kawai kuɗin scanning? Har tsawon shekara biyu baya Takawa da ƙafarsa!!

Fisabilillahi yanzu man lawan koda Ace ba Hausa Film yake yi ba Ai Abun a kalla a Taimake shi ne koma da ace lafiyarsa ƙalau.

Nasan man lawan lokacin yana karatun NCE a Sa’adatu Rimi College of education inajin set ɗinsu sun kammala ne a 2017/2018 mu kuma mun kammala 2018/2019 muna yawan haɗuwa Dashi wanda na sami labari ko Acikin makaranta malamai suna Taimakonsa wajen karatu da wasu Abubuwa saboda yadda Allah ya halicce shi ba kowane irin Aiki zai iyayi ba, Amma kuma yanada ƙoƙarin karatu.

Nayi nazari kuma na tabbatar wa da kaina sana’ar Film ɗin Hausa wallahi ba sana’ar Arziƙi bace.

Man lawan Allah yabaka lafiya ya kuma chanza ma da Abinda yafi sana’ar Film Alkhairi Ameen Ameen.

✍️
Shehu Tijjani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button