Uncategorized

HARIN DA AKA KAI A COCI: Bai Kamata A Kaiwa Yan Arewa Hari Ba- Shehu Sani

Kisan Kisan Owo: Bai Kamata A ci zarafin Yan Arewa Mazauna Kudu Ba_ Shehu Sani

Daga Comrade Yusha’u Garba Shanga.

Biyo bayan wani mummunan hari da wasu ‘yan ta’adda suka kai wa mabiya Coci a garin Owo na jihar Ondo, tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi gargadi kan cin mutuncin ‘yan Arewa mazauna Kudu.

Shehu Sani ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin din da ta gabata ta shafinsa na Twitter, inda ya ce manufar ‘yan ta’addar ita ce ta haifar da barna da rigingimun kasa.

“Manufar wadancan ‘yan ta’adda ita ce ta haifar da fitina da rigingimun kasa. Ba su keɓe masu bauta a cikin masallatai ko a cikin majami’u.

“Arewa ce ke fama da tashin hankalinsu a kullum. Bai kamata a ci zarafin ’yan Arewa mazauna kudu ba saboda munanan ayyukan wadannan ‘yan ta’adda,” ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A baya dai Sanata Shehu Sani ya yi Allah-wadai da harin da aka kai a cocin Katolika na Ondo, inda ya bayyana shi a matsayin wani mummunan aiki na ta’addanci, da dabbanci da kuma abin da ya kamata a yi la’akari da shi.

“Dole ne dukkan ‘yan Najeriya su hada kai wajen yin tir da wadanda suka aikata wannan danyen aikin. Dole ne a yi duk abin da za a gabatar da maharan. Ya isa wannan zubar da jini,” ya rubuta.

Al’amarin da ya faru a Cocin Owo, wanda shi ne hari na baya-bayan nan a Najeriya, na ci gaba da yin tofin Allah tsine daga ciki da wajen kasar, inda ake ta kiraye-kirayen hukumomi da su yi abin da ya kamata wajen kare martabar rayuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button