Uncategorized

BIDIYO: Nesa Tazo Kusa Ku Kalli Bidiyo Dakuma Hotunan Kafin Aure Na Pree Wedding Din Lilin Baba Da Ummi Rahab

BIDIYO: Nesa Tazo Kusa Ku Kalli Bidiyo Dakuma Hotunan Kafin Aure Na Pree Wedding Din Lilin Baba Da Ummi Rahab

“Ranar kuke jira yau gashi tazo Muma da tamburan mu gashi munzo Ango muke yi wa shida amarya Muyo rawa ta murna anyi aure”.

Wannan dai wani bangare ne na cikin wakar Umar M Sharif wanda yayi daidai da wannan labarin namu.

Kwance tashi lokaci yazo, yanzu dai gaba daya saura kwanaki 14 a daura wannan aure na Lilin Baba da Ummi Rahab, kamar yanda katin daurin aure ya fita.

Ummi da Lilin Baba dai basu dade da fara soyayya ba, sai dai babu inda labarin soyayyar tasu bai shiga ba saboda yanda suke nuna wa junan su so da kauna a kafafen sadarwa na zamani.

Wanda sanarwar daurin auren nasu yazowa wasu a bazata, kasancewar ba’a cika yin irin wannan auren a kannywood ba.

Da yawa wasu jaruman kansha soyayya kaman zasu cinye junan su, sai daga baya kuma a jisu shiru ba batun soyayya ba maganar auren.

Ga dai cikakken rahoton nan a kasa, akan batun auren.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button