Uncategorized

BIDIYO DA DUMI-DUMI: Yan daba sun kai wa al’ummar Hausawa hari a Ondo, bayan da ‘yan ta’adda suka kai hari coci

’yan daba suka kai wa al’ummar Hausawa hari a Ondo, bayan da ‘yan ta’adda suka kai hari coci, harma suka kashe masu ibada –A Cewar Shugaban karamar hukumar.

Inda Ya Kara Da Cewa Wasu ‘yan ta’adda da aka zargin yan fulani ne suka kai wa mabiya cocin hari a yayin gudanar da ibada a ranar lahadi.

Kamar Yadda Jaridar Sahara Repoters Ta Rawaito A ranar Lahadin da daddare ne wasu mazauna yankin suka far wa wasu ‘yan Arewa a yankin Ogwatoghose da Ikare na jihar Ondo a matsayin ramuwar gayya kan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai cocin Catholic da ke kan titin Owa-luwa a karamar hukumar Owo ta jihar.

‘Yan ta’addan dai sun harbe da yawa daga cikin jama’ar yankin. Daya daga cikin faifan bidiyon lamarin da Kafar Sadarwa Ta Sahara Reporters ta samu ya baiyana cewa an kashe mata da yara da dama a harin.

Wani basarake a garin Owo, inda lamarin ya faru, ya ce wasu mazauna garin sun mayar da martani inda suka far wa wasu Hausawa yan Arewacin Najeriya) a wasu yankunan garin.

Sai dai an bayyana maharan a matsayin ’yan bata-gari kuma marasa galihu wadanda kawai suke amfani da irin wannan damar wajen wawure dukiyar jama’a.

Rahotanni sun baiyana cewa, “Akwai wurin da Hausawa suke saye da sayar da kayan aluminium da ƙarfe. An yi musu duka tare da lalata musu kayansu.

Hakan ya faru ne a Titin Ogwatoghose (Owatowse). “Ba a samu damar kwasar ganima ba. Haka zalika an kai wani harin harin makamancin wannan a unguwar mahadar Ikare.

“Wasu daga cikin maharan bata gari ne. A gare ni, waɗannan mutane ne marasa galihu da suke yi wa kansu hidima.”

Ga Karin Bayani Game Da Lamarin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button