Uncategorized

BIDIYO: Kwankwanso Ko Jahar Kano Bazaici Ba A Zaben 2023 Saboda Bashi Da Magoya Baya A Yanzu Inji Ganduje.

Kwankwanso Ko Jahar Kano Bazaici Ba A Zaben 2023 Saboda Bashi Da Magoya Baya A Yanzu Inji Ganduje

Ko a iya jihar Kano Kwankwaso bazai kai labari ba, ballantana kuma azo maganar Nigeria — Ganduje.

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yasha alwashin cewa, tsohon mai gidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda yake takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, bazai kai labari a Kano ba ballantana Nigeria a zaɓen 2023.

Ganduje ya bayyana haka ta cikin wata hira da yayi a TVC a yammacin yau, inda yace ba wannan ne karon farko da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yake tsayawa takara amma yake gaza yin nasara ba.

Har ila yau, Ganduje yace son kan Kwankwaso wata dama ce da jam’iyyar APC zata samu nasara a babban zaben 2023, kuma musamman yanzu da bashi da goyon bayan Atiku Abubakar, dukda dai ko a bayan ma da yake da goyon bayansa, sun kayar dashi harda Atikun, a cewar Ganduje.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button