DA DUMI-DUMI: Mutane da dama ne suka mutu sakamakon fashewar bam a wani cocin Ondo a ranar Lahadi, yayin da Kiristoci Suke gudanar da ibada.

Mazauna garin sun shiga cikin fargaba bayan da wani bam ya tashi a cocin St Francis Catholic da ke titin Owa-luwa a karamar hukumar Owo ta jihar ranar Lahadi.

Kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito, wasu masu gudanar da ibada sun rasa rayukansu sakamakon lamarin.

Fashewar, rahotanni sun ce ta afku ne a harabar cocin a lokacin da jama’a ke ci gaba da gudanar da taron.

Lamarin ya haifar da barkewar Fargaba sosai a yankin yayin da mazauna unguwar da ke yankim suka gudu domin tsira da rayukansu.

Har ila yau an ce an dakatar da harkokin kasuwanci da zamantakewa a garin.

Wata majiya kuma ta ce wasu makiyaya ne da ake zargin sun kai hari coci tare da kashe masu ibada.

A cikin wani faifan bidiyo da aka yi a shafin yanar gizo na Twitter, an ga gawarwakin masu bautar da ba su da rai a kwance a cikin jini.

Click Here To Drop Your Comment