News

Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji’un!: Aƙalla Alhazai Tamanin Da Takwas 88 Ne Suka Rasu A Saudiya Wadanda Suka Fito Daga Bangladesh

Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji’un!: Aƙalla Alhazai Tamanin Da Takwas 88 Ne Suka Rasu A Saudiya Wadanda Suka Fito Daga Bangladesh

Aƙalla alhazan ƙasar Bangladesh 88 ne suka rasu a cikin watanni ɗaya da rabi da suka gabata a zamansu a ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.

Muhammad Maqsudur Rahman, Babban Shugaban Ofishin Haajjin Bangladesh a Saudi Arabiya, ya shaida wa manema labarai a yau cewa kashi 90 cikin 100 na wadanda suka rasu sun haura shekaru 60, yayin da biyar zuwa shida daga cikinsu basu kai shekarun ba.

Daga cikin wadanda suka rasu 77 maza ne, mata kuma 11, in ji Maqsudur.

Mafi akasarin tsofaffin alhazan sun rasu ne sakamakon bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki da kuma ciwon ƙoda, yayin da biyu suka mutu a wani hatsarin mota, shi kuma wani alhaji ya rasu sakamakon faɗowa daga wani tsauni da ke guraren ibada a garin Makka, inji Shugaban.

Da aka tambaye shi, Maqsudur ya ce tsofaffin alhazai, a mafi yawan lokuta, sun mutu ne sakamakon zaunannun cututtuka daban-daban a jikinsu da kuma sauran matsalolin lafiya.

Ya ci gaba da cewa, likitocin Bangladesh suna bayar da ayyukan kiwon lafiya ba dare ba rana ga dukkan alhazan kasar, inda ya ƙara da cewa kuma suna da adadin magungunan da ake bukata.

Maqsudur ya ce, an yi jana’izar dukkan wadanda suka mutu a kasar Saudiyya kamar yadda ‘yan uwansu suka buƙata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button