News

BIDIYO: Matan da ƴan bindiga suka yi wa fyaɗe a Katsina sun haifi ƴaƴa fiye da 500,000′

BIDIYO: Matan da ƴan bindiga suka yi wa fyaɗe a Katsina sun haifi ƴaƴa fiye da 500,000′

Binciken wasu dattawan arewacin Najeriya na cewa ƴaƴan da aka haifa sakamakon fyaɗe da ‘yan fashin daji ke yi wa mata a yankunan Katsina zuwa Zamfara sun kai rabin miliyan.

Ɗaya daga cikin shugabannin dattawan na Katsina, Dr Bashir Kurfi ne ya shaida haka a wata hira da ya yi da BBC, kan matsalar tsaro a yankunan arewacin Najeriya, musamman katsina da Zamfara.

Dr Kurfi ya ce binciken da suka aiwatar cikin shekarun da aka kwashe ana yaƙi da ‘yan fashin daji, ya tabbatar musu da wadannan alkaluma sakamakon rahotanni da suka tattara daga kauyuka.

Ya ce mata da dama na kawo ƙorafinsu da kuma bayanai kan irin mutanen da suke yi musu fyade.

Yankunan Batsari da Dutsenma da Kankiya da Chiranci da su Funtua, Safana da dai sauransu duk ana samun irin wannan matsala a Katsina.

Ya ce a baya kafin matsalolin tsaro sai motoci 20 zuwa 50 su je Kano a rana ko daga Sokoto zuwa Kano ko ƙasashen makwabta, amma yanzu an daina, ‘yan kasuwa sun daina tafiya saboda haɗari da ke tattare da hakan.

Dr Kurfi ya ce kafin soma bincikensu ko shiga harkar sa ido kan matsalolin tsaro, bayanai da dama a boye su ke, amma a yanzu da suke zama da ciyamomi da mutanen da ke wakiltar al’umma sun fahimci cewa akwai hanyoyin samar da sauki.

“Gwamnoni da dama na ɓoye batun ‘yan gudun hijira ba sa son ake maganarsu, kuma a kullum tada kauyuka ake yi, daruruwan mutane na rasa muhallansu.

“Gwamnati na ɓoye abun, ba ta son ake fadi. Galibi babu sansani don haka maƙale suke da ‘yan uwa da abokan arziki, in Dr Kurfi.

Sannan ya ce sun sha tuntuɓar gwamnatoci, wanda ba wai abu ne da basu sani ba, sai dai ba a samun biyan bukata amma kuma za su ci gaba da fafutika.

Wasu labaran masu alaƙa da za a iya karantawa

Dr Kurfi ya ce girman matsalar tsaro ta wuce tunanin mutane, domin shiga gida ake yi kai-tsaye a ɗauki mata har da na aure.

A wasu kauyukan ma ‘yan bindiga waya suke yi wa magidanta su ce su kawo musu matansu da yaransu ko kanwa.

Ya ce baya ga kashe-kashen da ake yi ana cin zarafin mata, ana aikata fyaɗen gungun a kansu.

“Akwai macen da wallahi maza sama da 40 ne suka yi mata fyaɗe.

“Sai su kai hari kan babura sama da 100 da manyan makamai, ga kwayoyin da suke sha, abin tambaya, ta ina suke shigo da irin wadannan miyagun abubuwa.”

‘Babu wani tsari da gwamnati ta fitar na taimaka mu su ko fitar da su daga ƙangi ko aƙuba ko mugun hali da suka tsinci kansu’

Dr Kurfi ya ce gaskiya akwai sakaci, domin batun sassanci da ake yi da ɓarayin ba ya haifar ɗa mai ido.

Sannan su waɗanda aka cutar, babu wani tsari da gwamnati ta fitar na taimaka mu su ko fitar da su daga ƙangi ko aƙuba ko mugun hali da suka tsinci kansu.

Dakta ya ce, akwai makarantu da dama a rufe wanda ‘yan bindiga suka mayar da su gidajensu, sannan wasu kauyukan ma tare suke rayuwa da ‘yan bindiga a cikin gidajensu.

“Za su ƙwace muku gonaki, su mayar da mutane bayi, a yi musu noma, su yi wa yaransu fyade.”

Dr Kurfi ya ce akwai rashin tsari abin da ke buɗe kofa har a samu damar kashe manyan jami’ai.

Babu wanda bai san maɓoyar manyan ɓarayin daji ba, har yawo suke cikin gari hankali kwance, in ji Dakta.

Ya kuma ce nasu aikin shi ne fadawa gwamnati abubuwan da suka lura da su, musamman nakasu, domin a gyara.

A cewarsa abin ba wai na kashe kuɗi ba ne, tsari ne kawai ake bukata da haɗin-kai tsakanin jami’an tsaro da kungiyoyin sa-kai domin cimma nasara.

Ya ce akwai alamar tambaya kan yadda ake tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya da kuma makudan kuɗaɗen da ake fitarwa wajen yaƙi da ‘yan ta’adda amma ba a ganin wani gagarumin sauyi.

Dr Kurfi ya ce ganin yadda abubuwa ke faruwa ne a yanzu haka suka bullo da tsarin aiki tare da jami’an tsaro ta yadda za su samar wa al’ummar jihar Katsina sauƙi.

Daga cikin dabarun da suka bullo da su har da daukar matasa 100 a kowacce karamar hukuma domin horar dasu a matsayin ‘yan sa kai ta yadda za su taimaka wajen kare al’ummar garuruwansu da kuma haɗa kai da jami’an tsaro wajen daƙile ayyukan ‘yan fashin daji.

Karin Bayani 👇👇👇👇👇👇👇

https://youtu.be/WlgmnMAaRJ4

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button