News

Innalillahi.. Bidiyon Yadda Yan Bindiga A Zamfara Suka Kwashe Mutane A Masallacin Juma’a

Innalillahi.. Bidiyon Yadda Yan Bindiga A Zamfara Suka Kwashe Mutane A Masallacin Muma’a

Yan bindiga dake garkuwa da mutane domin karbar diyya a Najeriya, sun kai hari a kauyen Zugu dake Jihar Zamfara inda suka kwahse mutane a Masallachin Juma’a.

Yan Bindigar Dai Sun Kwashe Mutanen Ne A Babban Masallacin Juma’ar garin wadanda suka je domin sauke farali.

Rahotanni sun ce Yan bindigar sun isa garin ne da misalin karfe 1 na rana a kasa, inda suka fara tattara mutane a Kasuwa, kafin daga bisani suka wuce Masallachin Juma’a suka kwashe masu jiran liman domin sauke farali.


Wani shaidar gani da ido a garin ya tabbatar mana aukuwar lamarin, yayin da yace jami’an tsaro cikin motoci guda 2 suna isa Zugun inda suka dauki wasu mutane 3 dan taimaka musu bin sawun barayin.

Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar matsalar tsaro sakamakon yadda Yan bindiga suka mamaye ta suna kai hari akan mutanen garuruwa daban daban.

Anan Muke Addu’ar Ubangiji Allah Ya Kubutar Dasu, Sukuma Wadannan Yan Bindiga Allah Ya Kawo Mana Karshen Su Amin

Ga Karin Bayani 👇👇👇👇

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button