Kannywood News

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un! Ashe Wannan Shine Dalilin Da Yasa Nafisat Abdullahi Tafita Daga Shirin Labarina

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un! Ashe Wannan Shine Dalilin Da Yasa Nafisat Abdullahi Tafita Daga Shirin Labarina

Kamar yadda kuka sani ne tuni akai nisa cikin daukar shirin nan mai dogon zango na labarina.

Wanda tuni daraktan shirin aminu saira ya baiyana maye gurbin jaruma nafisat abdullahi da jaruma fati washa.

Lamarin da yasa ayar tambaya a zuciyar yan kallo, duk da cewa hakan tasha faruwa acikin fina finai masu dogon zango ba iya shirin labarina kadai ba.

Sai dai abinda har yanzu mutane basu kai ga sani ba shine dalilin fitar jarumar daga shirin na labarina.

Sai dai a ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara, jaruma Nafisa Abdullahi ta wallafa takarda a shafin ta na Instagram inda ta sanar da cewa ta fice daga shirin sakamakon tarin ayyukanta da karatu da ya sha mata kai.

Jaruma Nafisa Abdullahi ta sanar da cewa fim din Labarina ya na daga cikin ayyukanta da ta ke alfahari da shi kuma kamfanin Saira Movies tamkar na ta ne saboda ta dade ta na aiki da kamfanin.

“Ina matukar jin zafin sanar da dukkanku cewa ba zan cigaba da aikin Labarina ba. Dalili shi ne rashin samun lokaci yadda ya kamata. Ina da kasuwanci na, makaranta, kamfanina da sauran fina-finai na da nake shirin fara dauka nan babu dadewa. “Ba zan ce a jira ni sai sanda na samu lokaci ba, dole za a cigaba da shirin Labarina ko da ni ko ba ni.

“Ina ba dubban masoya hakuri a kan fita ta daga shirin. Alakata da Saira Movies za ta cigaba da tafiya lafiya, babu hayaniya ko cin zarafi. Allah kuma ya ba su sa’a wajen kammala sauran shirin.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button