News

Innalillahi wa inna ilaihir raju’un;! Yadda Mahara Suka Shiga Har Cikin Gidansu Suka Kashe Matashi Har Lahira A Katsina

Innalillahi wa inna ilaihir raju’un;! Yadda Mahara Sun Shiga Har Cikin Gidansu Sun Kashe Matashi Har Lahira A Katsina

Wani rahoto da muke samu yanzu yanzu Daga Jamilu Dabawa, Katsina na cewa.

Wasu Mahara Dauke Da Makamai Sun Shiga Har Cikin Gidan Mahaifinsa Dake Unguwar Sha’iskawa A Karamar Hukumar Musawa Ta Jihar Katsina.

Inda Suka Kashe Matashi Mai Suna Muhammad Abubakar Usman Har Lahira A Daren Jiya Alhamis.

Kamar Yadda Majiyar RARIYA Ta Nakalto Cewa Cewa Maharan Sun Samu Damar Kutsawa Gidan Dakta Abubakar Usman, Wanda Likitan Dabbobi Ne.

Kuma Darakta Ne A Ma’aikatar Noma Da Albarkatun Kasa Na Jihar Katsina Dake Unguwar Sha’iskawa A Cikin Garin Musawa Da Misalin Karfe 9:30 Na Daren Jiya Alhamis.

Kuma Anan Sun Yi Amfani Da Makamai Masu Karfi Wajen Yin Wannan Aika-aikar.

Tuni Dai Aka Yi Jana’izarsa Kamar Yadda Addinin Musulunci Ya Tanada A Garin Musawa Da Safiyar Yau Juma’a.

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button