Kannywood NewsentertainmentNews

Jaruman Kannywood Na Cigaba Da Jin Jinawa Gwamna Ganduje Akan Abduljabbar

Har Yanzu Jaruman Kannywood Na Cigaba Da Da Yabawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Kan Matakin Da Ya Dauka A Kan Sheikh Abduljabbar.

Film Din Da Jarumin Ya Taba Yi
Daya Daga Cikin Film Din Da Jarumin Ya Taba Yi

Tun Bayan Da Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje Ya Dakatar Da Sheikh Abduljabbar Daga Yin Wa’azi Dakuma Yin Karatuttuka Kamar Yadda Ya Saba.

Biyo Bayan Kararsa Da Wasu Daga Cikin Malaman Jahar Kano Sukai Na Zargin Cewa Karatuttukan Malamin Ka Iya Tayar Da Zaune Tsaye.

Dayawan Mutane Suka Fito Suna Jinjinawa Gwamnan Tare Da Yaba Masa Akan Wannan Matakin Da Ya Dauka.

Ciki Kuwa Harda Wasu Daga Cikin Jaruman Shirya Fina Finan Hausa Na Kannywood.

Dafarko Dai Mawaki Naziru M Ahmad Ne Ya Fara Yin Tsokaci A Cikin Wani Guntun Bidiyo Da Ya Wallafa A Shafinsa Na Sada Zumunta.

Wanda Har Mawakin Ya Bayyana Cewa Ko Shi Yafi Sheikh Abduljabbar Din Ilimi. Wanda Daga Karshe Ya Fashe Da Kuke.

Mutane Da Dama Sun Zargi Mawakin Da Kukan Munafarci A Gefe Guda Kuma Wasu Suka Yaba Mai.

Jarumi Ali Nuhu Tare Da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje
Jarumi Ali Nuhu Tare Da Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje

To Sai Dai A Yau Ma An Samu Wani Jarumin Da Ya Sake Fitowa Ya Jin Jinawa Gwamna Ganduje Kan Wannan Matakin Da Ya Dauka.

Jarumin Mai Suna Sukairaju Yusif Ahli. Wanda Akewa Lakabi Da Sk_Na_Allah Ya Bayyana Hakan Ne Acikin Wani Guntun Video Da Ya Wallafa A Shafinsa Na Instagaram Da facebook

Jarumi Ali Nuhu Tare Da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button