Kannywood News

Jarumi Ali Nuhu Ya Bayyana Bidiyon Matashin Ɗansa Dake Buga Kwallo a Ingila, Ya Birge Jama’a

Jarumi Ali Nuhu Ya Bayyana Bidiyon Matashin Ɗansa Dake Buga Kwallo a Ingila, Ya Birge Jama’a

Kamar Yadda Zaku Kalla Acikin Bidiyon Dake Kasa, Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, mahaifi ne mai alfahari da dan shi wanda ya bayyana Ahmad a matsayin kwarrren dan kwallon kafa.

Ali Nuhu ya bayyana hoton matashi Ahmad wanda ke shirin fita filin wasa a wani wasan da zasu yi a Ingila a shafinsa na Instagram.

Jarumin ya yi wa ‘dansa fatan alheri, kuma ‘yan Najeriya sun dinga kururuwa zuwa sashin tsokaci inda suke bayyana birgesu da yayi.

Jarumi Ali Nuhu ya wallafa hotunan, tare sa yin wasu kalamai masu cike da karfafa gwiwa ga dan nasa.

Ba wannan ne karo na farko da jarumin ke kai kawo ba, na ganin cewa dan nasa ya samu kulob din buga ball a kasar waje.

Sai a wannan karon Allah Ya isa nufi ya cika musu muradin su na samun kulob din buga ball.

Kuma Ahmad Ali Nuhu Nadaga cikin wadanda aka zaba su gwada baiwar su dan tantancewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button