Kannywood News

Na Taba Yin Mafarkin Kabarina Na Ci Da Wuta A Lokacin Da Nake Harkar Fim, Cewar Jarumar Finafinan Indiya, Sanah Khan

Na Taba Yin Mafarkin Kabarina Na Ci Da Wuta A Lokacin Da Nake Harkar Fim, Cewar Jarumar Finafinan Indiya, Sanah Khan

An yi hira da jarumar da ta yi ritaya daga harkar finafinan Indiya, wadda kuma ta gabatar da aikin hajjin ta na farko a wannan shekarar, wato Sanah Khan.

Inda ta bayyana cewa duk da cewa tana samun duk wani abin kyale-kyalen duniya tun daga kan kuɗi da daukaka.

Sannan tana iya yin duk abinda ta ga dama, amma saidai ta rasa abu guda daya shine kwanciyar hankalin rai.

Kwatsam wani lokaci a cikin shekara ta 2019 cikin watan Ramadan ta yi mafarki kabarin ta yana ci da wuta bal-bal.

inda ta ce wannan abu ya yi matukar tayar mata da hankali, shi ya sa ta yi gaggawar watsar da duk wani kyale-kyalen duniya ta zaɓi saka hijab.

Sannan ta bar harkar fim daga karshe ta yi aure kuma gashi yanzu Allah ya temaketa ta gabatar da aikin Hajji tare da mijinta, Malamin addinin musulunci ne.

Duk wannan hirar ta dora bidiyon a shafinta na sadarwa.

Daga Nanerh Hawwer

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button